بسم الله الرحمن الرحيم, وصلي الله علي سيدنا محمد وعلي أهله وصحبه وسلم
A wannan duniyar tamu kullum muna samun sababbin abubuwa naci gaba, imma wanda yadace da yardar addininmu kokuma sabanin hakan. To amma ga wanda yake da wayewa ta addinin musulunci yasan cewa duk wani cigaba ko wata fasaha da wayewa matukar yasabawa shari'ah to yatashi daga sunan wayewa/cigaba yakoma gidadanci da ci baya.
Amma kuma a wadansu lokutan makiyanmu (yahudu da nasara) sukan kirkiro wadansu abubuwa da niyyar shagaltarda al'ummar musulmi amma kuma bisa hikima da fasahar da Allah sai yahorewa musulmi damar canja akalar wannan abin yakoma mai ampani awajensu dakuma addininsu.
Asalin shafin facebook ance anqirqiroshi ne domin sada zumunta, shiyasama koda awajen kara abokanai(adding friends) ake ampani ka kalmar 'people you may know'.
Amma daga baya bayan da al'umar musulmi suka tsunduma cikinn harkar sai sukayi kokarin musuluntarda harkar tahanyar yin rubuce rubuce irin na fadakarwa da wa'azatarwa bisa tsari na addiin musulunci.
Faruwar hakan ne yabawa wada da basu sami wannan fahimfar ba dama domin suma su shiga a dama dasu. Sai yazanamanto a halin yanzu idan kadube shafin facebook zakaga mafi yawancin abubuwanda zaka gani shine rubututtukan jama'ar musulmi na kungiyoyi da dariqu daban daban.
Kasancewata daya daga cikin irin wadannan masu lekawa shafin facebook, na fahimci wasu matsaloli da al'umarmu suke fuskanta gameda wannan matashiyar tawa.
Daga cikin matsalolinda nakeson yin Magana akansu sun hada da:-
1: Rashin tsarkake niyya yayin rubutu.
2: Rashin samun cikakkiyar madogara gameda abinda mutun yakeso ya rubuta
3: Rashin hikima wajen isarda sakon
4: Rashin karanta rubutun wanda muke da adawa dashi da manufa mai kyau.
Wadannan sune kadan daga cikin matsalolinda muke fama dasu a wannan yanayin da muke ciki. Kuma sune zan dauka daya bayan daya nayi bayani akansu iyakar abinda Allah yahore min na fahimta. Ina rokon Allah yabani muwafaqa da ikhlasi wajen bayanin nawa.
1:-RASHIN TSARKAKE NIYYA YAYIN RUBUTU:
Dafarko ma dai sanin kowane cewa har aragowar ayyukan ibada na musulunci Allah baya amsarsu kuma yabada lada har sai idan wannan aikin wacika sharadin da ake nema kafin a amshi aikin mutum, sharuddan kuwa guda biyu ne,
A: IKHLASI: shine kayi abu domin nemar yarda Allah shikadai ba tare da neman yarda ko birgewa awajen wanin Allah ba.
B: MUTABA'A: shine kayi aikin irin yadda shari'ah tayi umarni, bawai kaje kazabi hanya ba wadda batada rijista daga ofishin shugaban halittun sammai dana kassai (SAW).
Toh kaga kenan rubutunka bashida wani ampani matukar kayishine ba domin Allah ba. koda kuwa mai karubuta, kuma komai yawan wadanda suka amfana da abin.
Sanna rashin tsarkake niyya yayin rubutu shine yake kai mutum ga yiwa wani sharri, ko kazafi ko kokuma yada abinda inka kulle mutum kace yakare kansa toh wallahi bashida hujjojinda zai iya kare kansa dasu.
Sannan sanin kowane cewa duk wanda yakeyin ayyukansa batare da tsarkake niyya ba (ikhlasi) toh ba makawa shaidan zai yi galaba akansa. Zamu sami hakan ne a yayinda Allah Madaukaki yake Magana da iblis la'ananne, bayan yayi girman kai ga barin yin sujjada da ubanmu annabi Adam.
Allah yace:-
إلا عبادك منهم المخلصين
ma'ana: saidai kawai bayinka wadanka suke da ikhlasi (wadanda suke tsarkake niyyarsu yayin aikin ibada).
Toh kaga kenan yakamata kazamanto duk abinda zakayi ka dinga tsarkake niyyarka kayi domin Allah, sai ka sami ampani biyu, daya aduniya dayan kuma a lahira. Dama Allah yayi umarni ne kawai abauta masa tareda ikhlasi. Allah yace:-
وما أمرو إلا ليعبد الله مخلصين له الدين حنفاء ويقيم الصلاة ويؤتو الزكاة وذالك دين القيمة
Ma'ana; Allah yace bai yiwa bayinsa umarni ba sai domin su bauta masa shikadai, suna masu tsarakake ibada, kuma su tsaida sallah sannan su bayarda zakkah, hakan shine addinin gaskiya kuma mikakkke.
Idan kace wa'azi kakeyi har kana tinkaho toh kasani cewa indai har bakayi domin Allah toh da abinda kakeyi da babu duk daya, garama kayi don Allah ko kaci riba.
2 RASHIN SAMUN CIKAKKIYAR MADOGARA GAMEDA ABINDA MUTUM YAKESO YARUBUTA:-
koda kanaso kayiwa al'umma wata nasiha ne toh yakamata yazamanto kanada ilimi gameda abinda kake so kayi bayani akai. Rashin samun wannan ne yake sawa mutun yayi rubutu amma idan wani abu yashige maka duhu katambayeshi saikaga bazai iya kare kansa ba. itaa da'awa Allah ne yayi umarni da ita amma fa ba cewa yayi kayita kota halin kaka ba, cewa yayi sai kanada ilimi da hujja
Allah yace
قل هذه سبيلي أدعو إلى الله على بصيرة أنا ومن اتبعني وسبحان لله وما أنا من المشركين
Ma'ana: Allah yake bawa annabinsa umarni ya gayawa al'umarsa cewa shi wannna itace hanyata(musulunci) kuma ina kira zuwaga addinin Allah, bisa ilimi muke dani da wadanda suka bini, tsarki yatabbata ga Allah kuma ni bana daga cikin masu hada shi da kowa wajen bauta. Kaga kenan annabi ya fada cewa shima da'awar da yakeyi yana yintane bisa ilimi.
3: RASHIN HIKIMA WAJEN ISARDA SAKO:
koda sakon da kake dauke dashi gaskiya ne, toh fa dole sai kasan yadda zaka isarwa da wanda kakeson isarwa sakon naka ta hanya mai kyau, rashin iya isarda sakon ne yasa wani lokacin mutun zaiyi rubutu amma arasa wanda zai yarda ya karbi sakon nashi, watakila saboda rashin tausasan lafuzza.
Yakai dan uwa kasani cewa yayinda kakeson yin da'awa to akwai wani muhimmin abu dayakamata kafara ganewa.
* kasani cewa su mutane batattu kala biyu ne
A)akwai wanda yabata bisa son zuciya; toh shi wanna shi ake yiwa wa'azi zafi zafi
B)akwai kuma wanda yake bin abin abisa rashin sani, to idan zaka yiwa wannan wa'azi akwai bukatar ayi mai acikin sanyin zuciya, saboda shima dayasan bata ne da bazai bi ba.
toh yakamata mu dinga la'akari da wanda zamuyiwa nasiha.
Allah yace
ادع إلي سبيل ربك بالحكمة والموعظة الحسنة
Ma'ana: kayi kira zuwaga bin hanyar ubangijinka (addinin musuluncin) amma kayi ampani da hikima wajen da'awa. Ita kuma hikima itace yin zafi a inda yakamata dakuma yin sanyi a inda yakamata.
4: RASHIN KARANTA RUBUTUN WANDA MUKE ADAWA DASHI DA KYAKKYAWAR NIYYA:-
wani lokacin idan wanda muke adawa dashi yayi rubutu to yawancinmu bamu tsayawa mu karanta da kakkyawar niyya, hakan kuma yanada illa saboda koda yayi daidai toh fitilar zuciyarmu bazata haska mana mugani ba, sannan wani wajen ma daidai mutum zaiyi amma saika fahimci abin kamar kuskure yayi. Shikuwa idan kanaso kaci riba da mutum to idan yayi rubutu sai kayi niyyar karantawa da kyakkyawar niyya, hakan ne zaisa idan yayi daidai sai zuciyarka tayi saurin yarda, idan kuma yayi kuskure sai ka gyara masa ta hanyar data dace.
Rashin cika wannan qa'idar ne yakesawa idan kayi rubutu kawai saiwani yakaranta bada kyakkyawar niyyaba sai kaji yana maka raddi akan abinda kai ba haka kake nufi ba. kuma kayi kayi dashi amma yakasa ganewa sakamakon tun farko baiyi niyya maikyau ba.
Wadanna sune abubuwanda idan muka bisu zamuci ribar shiga shafin facebook aduniya watakilama har a lahira. Kuma mukaru da ilmomi daban daban daga wajen wadanda muke da aqida iri daya dakuma wadanda muke da bambancin aqida dasu.
Allah yabamu ikon gyarawa. Allah yasa mudace ameen.